1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo karshen zaben Indiya

May 19, 2019

An kawo karshen zaben da aka dauki makonni bakwai ana yi a kasar Indiya da mazabar Firaminista Narendra Modi ke neman sabon wa'adi na shekaru biyar nan gaba.

https://p.dw.com/p/3Ik5K
Indien Parlamentswahlen | Hinduistische Heilige vor Wahllokal in Kalkutta
Hoto: Reuters/R. De Chowdhuri

Sama da Indiyawa miliyan 100 da ke yankin mazabar Varanasi ta Firaminista Narendra Modi, suka kalmashe zaben kasar da aka fara cikin watan jiya.

Firaminsta Narendra Modi, na neman ci gaba da mulki na sabon wa'adin shekaru biyar a babbar kasar da ta fi kowacce girman dimukuradiyya a duniya.

Mazabar ce dai ta tula wa Firaministan kuri'un da suka ba shi rinjayen hawa karaga a shekarar 2014.

A ranar 23 ga wannan watan ne kuwa za a fara lasafta kuri'u a zaben na Indiya.