1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An koma filin daga a Sri Lanka bayan rugujewar taron zaman lafiya

November 1, 2006
https://p.dw.com/p/Budj

Rundunar sojin sama ta Sri Lanka ta kai harin bam akan wuraren ´yan tawayen Tamil Tigers dake gabashin kasar mai fama da rikici. Wannan harin ya zo ne a lokacin da ake kara nuna fargabar tabarbarewar rigingimu a kasar bayan rugujewar shawarwarin samar da zaman lafiya kwanaki 3 da suka wuce. Harin da aka kai a gundumar Batticaloa na gabashin kasar ya zo ne yayin da ake kai hare hare da bindigogin atileri da rokoki a yankunan arewa da gabashin wannan tsibiri. Ba wani labari game da asarar rayuka. A yau da safe ´yan tawaye sun ta da wata nakiyar karkashin kasa a gundumar Vauniya dake arewacin kasar inda suka halaka farar hula daya sannan su kuma sojin ruwa suka nitsa da wani kwale-kwalen ´yan tawaye a can gabar teku dake arewa maso yamma.