1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kulla wasu yarjeniyoyi a tsakanin Zimbabwe da Afrika ta kudu

November 17, 2005
https://p.dw.com/p/BvKd

Gwamnatin kasar Zimbabwe data Africa ta kudu sun cimma yarjejeniyar inganta harkokin tsaro da musayar bayanin sirri a tsakanin su.

Cimma wannan yarjejeniya dai tazo ne a dai dai lokacin da wasu kasashe a duniya keci gaba da yin Allah wadai da gwamnatin kasar ta Zimbabwe.

Da yawa dai daga cikin kasashen na yamma na sukar gwamnatin ta Mugabe ne da hannu a game da tabarbarewar tattalin arzikin kasar a hannu daya kuma da take hakkokin yan adam.

´A waje daya kuwa Ministan ma´aikatar leken asiri na Afrika ta kudun wato, Ronnie Kasrils yabawa mahukuntan na Zimbabwe yayi da cewa sunyi namijin kokari wajen ciyar da kasar gaba a fannoni daban daban na rayuwar bil adama, a tsawon shekaru 25 da samun yancin kai daga kasar Biritaniya.