An amince da yarjejeniyar sulhu a Libiya
December 17, 2015Talla
Wakilan da suka futo daga cikin majalisar kasar da ke adawa da juna sun sanya hannu ne a kan jadawalin tsarin karba-karba a gaban mai sanya idanu na Majalisar Dinkin Duniya Martin Kobler gami da jami'an diplomasiya a kasar Moroko.
An dai samun nasarar kulla yarjejeniyar ce a tsakanin bangarorin biyu na kasar Libiya da ta sha fama da zub da jani bisa sanya hannun Majalisar Dinkin Duniya