1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Samun daidaito tsakanin gwamnatin da 'yan kwadago

September 12, 2019

An kama hanyar kai karshen rikicin karin albashin ma'aikata da aka dade ana yi a Najeriya bayan da gwamnatin kasar ta ce ta kafa kwamitin da zai kammala aiki bisa sabon albashin.

https://p.dw.com/p/3PVDn
Nigeria Arbeiterkongress protestiert 2010
Hoto: dapd

Duk da cewar dai tun cikin watanni biyar da suka wuce Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya rattaba hannu bisa dokar karin albashin, ana shirin kare shekarar bana cikin halin ja-in-ja tsakanin ma'aikatan kasar da ke zargin mahukunta da jan kafa,da kuma gwamnatin da ke cewar an kusa kawo karshe. Baki dai ya zo daya tsakanin gwamnati tarayyar da jihohi dama kungiya ta masu daukar aikin game da sabon mafi karancin albashin Naira 30,000. Abin jira a gani dai na zaman kaiwa ga murmushin ma'aikatan tarrayar Najeriyar da ke zaman na baya ga dangi a cikin yanki na yammacin Afirka a kan batun albashin.