1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An naɗa firimiyan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Usman ShehuMarch 27, 2013

Nicolas Tiangaye aka sake baiwa muƙamin Firayim minista a sabuwar gwamnatin da 'yan tawayen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya za su kafa

https://p.dw.com/p/185GH
Seleka rebel coalition members, which launched a major offensive last month, hold on January 10, 2013 a position in a village 12 kms from Damara, where troops of the regional African force FOMAC are stationned. Three-way peace talks between the Central African government, the rebel coalition that conquered much of the country over the past month and the political opposition began on January 9 in Gabon. With a lightning advance starting December 10, the rebels took over most of the Central African Republic. They are demanding that Central African President Francois Bozize step down, but the head of state, who took power in a 2003 coup, warned on the eve of the talks that he would not leave his job. AFP PHOTO/ SIA KAMBOU (Photo credit should read SIA KAMBOU/AFP/Getty Images)
Yan tawayen Seleka da suka karɓi iko a Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: AFP/Getty Images

Jagoran kifara da gwamnati a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, ya naɗa Nicolas Tiangaye a matsayin firamim minista. Tiangaye wanda dama can 'yan tawayen suka bada shi ga toɓeɓɓen shugaba Bozize, da ya zama firayim minista a wata gwamnati haɗaka da bata kai ko'ina ba, yace sabon shugaban ya amince masa da ya ci gaba da muƙaminsa ƙarƙashin sabuwar gwamnati. Micheal Jotodia, jagoran yan tawaye da suka karɓi iko ranar Lahdi da ta gabata, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa, yace zai yi aiki tare da Tiangaye a matsayin firayim minista.

Rohotanni dai su bayyana cewa, tun bayan wannan juyin mulki, mazaunan birnin Bangui babban birnin ƙasar musamman 'yan zamna gari banza, suke ci gaba da wasoson ganima.Tuni sun wawashe da dama daga shaguna da kuma gidajen wasu masu hannu da shuni. Sojojin Seleka sun yi yunkurin magance kwasar ganima, to amma har yanzu ba su cimma nasara ba, inji Patrice Zemoniaka wani dan jarida dake zaune a birnin Bangui.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasir Awal