1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nada Ibn Chambas a matsayin jagoran rundunar samar da zaman lafiya a Dafur

December 21, 2012

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afrika ta AU sun bayyana sunan Mohamed Ibn Chambas a matsayin jagoran rundunar tabbatar da zaman lafiya a yankin Dafur.

https://p.dw.com/p/177aM
Mohamed Ibn ChambasHoto: AP

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon da takwararsa ta kungiyar kasashen Afrika ta AU Nkosazana Dlamini Zuma ne su ka shaida hakan a wata sanarwa da su ka fitar da maraice jiya Alhamis.

Shugabannin sun ce nada Mr. Chambas a matsayin shugaba rundunar ta wanzar da zaman lafiya wadda ta fi kowacce girma a duniya na da nasaba da irin kwarewar da Chambas din ya ke da ita a matsayinsa na jami'in diflomasiyya.

Tuni dai jami'an diflomasiyya a nahiyar Afrika su ka yi na'am da wannan sabon matsayin da aka ba Chambas din inda galibinsu ke cewar ya na da dukannin ilimi da kuma kwarewar da ake bukata wajen aiwatar da aikin.

Mwallafi : Ahmed Salisu
Edita : Yahouza Sadissou Madobi