1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nemi yanke hukuncin kisa ga wani ɗan adawan Saudiyya

Usman ShehuMarch 27, 2013

Wani fitaccen mai adawa da gwamnatin Saudiyya na iya fiskatar hukuncin kisa, kamar yadda masu shigar da ƙara suka nemi a yi.

https://p.dw.com/p/1852r
Saudi new King Abdullah listens to a tribal chief as he receives oaths of loyalty from hundreds of top Islamic clerics, tribal chiefs and other prominent Saudis on Wednesday Aug.3, 2005, in a traditional Islamic investiture ceremony that bestows his legitimacy
Sarki Abdullah na Saudiyya ke sauraron shawara a wani taron da aka yiHoto: AP

Masu gabatar da ƙara a ƙasar Saudiyya sun nemi a yanke hukuncin kisa ga malamin da ya jagorancin yi wa gwamnati bore tamkar wanda ke faruwa a sauran ƙasashen Larabawa. Sheikh Nimr-Al nimr wanda ake ganin mai tsattsauran ra'ayi ne da ya fito daga yan Shi'a marasa rinjaye a Saudiyya, ya bayyana kotu a yau Ltinin, wanda shine karon fargo da aka gan shi tun watan Julin bara da jami'an tsaro suka kama shi. Ƙasar Saudiyya wanda yanzu haka ke kan gaba a marawa yan tawayen Siriya don su kiraf da gwamnati, lawyoyin ta suka ce neman a yi wa gwamnati bore wanda Shehin ya yi, tamkar yaƙi da Allah ne, don haka kamata ya yi a yanke masa hukuncin kisa bisa tsarin sharin musulunci. Yan sanda da masu adawa da gwamnatin sun yi ta artabu a ƙasar Saudiyya, musamman a yankin da yan Shi'a suka fi ƙarfi. Boren ana yinsa ne tun kusan shekaru biyu da aka fara zanga-zanga neman kafa mulkin demokraɗiyya a ƙasashen larabawa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Mohammed Abubakar