1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da kwamitin da zai tattauna da Boko Haram

April 24, 2013

Wannan dai na zaman kama hanyar buɗe sabon babi a cikin rikicin rashin tsaro a Najeriya, da ya yi sanadiyar mutuwar dubun muitane a cikin shekaru uku.

https://p.dw.com/p/18Mjp
PRESIDENT GOODLUCK JONATHAN (5TH L) ; VICE-PRESIDENT NAMADI SAMBO (6TH L) WITH MEMBERS OF THE COMMITTEE ON DIALOGUE AND PEACEFUL RESOLUTION OF SECURITY CHALLENGES IN THE NORTH AFTER THEIR INAUGURATION AT THE PRESIDENTIAL VILLA ABUJA ON WEDNESDAY (24/4/13).
Hoto: DW/A. Ubale Musa

A wannan Larabar shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya rantsar da wani kwamitin mutane 25 da ya dora wa alhakin tattaunawa da 'ya'yan kungiyar Boko Haram masu fafutuka da bama bamai.

Babu dai zato ba kuma tsammani fadar gwamnatin kasar ta ce ta sauko daga dokin naki ta kuma ce a shirye take domin tattaunawa da 'ya'yan kungiyar da ake wa lakabi da Boko Haram da suka kai ga ta da hankali suka koma dora tarayyar ta Najeriya bisa taswirar kasashen dake takama da ta'addanci a cikinsu.

Kwamitin kuma da gwamantin kasar ta ce ta bai wa tsawon watanni uku domin jan aikin da ke iya sauya halin da kasar ke ciki da kuma su kansu gwamantin kasar suka tabbatar da girman sa.

CROSS SECTION OF MEMBERS OF THE COMMITTEE ON DIALOGUE AND PEACEFUL RESOLUTION OF SECURITY CHALLENGES IN THE NORTH DURING THEIR INAUGURATION AT THE PRESIDENTIAL VILLA ABUJA ON WEDNESDAY (24/4/13).
Hoto: DW/A. Ubale Musa

Kwamitin kuma da shugaban kasar ya kaddamar a wannan Laraba cikin fata da ma tunanin siddabaru da nufin ganin bayan rikicin da ya gagari karfi da dabarun mahukuntan kasar.

"Duk 'yan Najeria na saran wannan kwamiti ya yi duk wani siddabaru, kuma muna rokon Allah Ya basu basirar yin haka", inji shugaba Jonathan sannan sai ya ci gaba da cewa. "In ba zaman lafiya ba za mu iya ayyukan ci gaba ba komai kudurin mu. In ba zaman lafiya ba za mu ci gaba ba a matsayin kasa ba."

Kwamitin na da manyan ayyuka gabansa

Wannan kwamiti zai kaddamar da tattaunawa da 'yan kungiyar Boko Haram, na biyu kuma zai dubi hanyoyin ajiye makamai sannan kuma da batun yin afuwa ga kungiyar.

Sabon kwamitin dai na zaman yunkuri na baya baya a kokarin kawo karshen rikicin dake zaman irin sa mafi girma cikin kusan shekaru 40 din da suka gabata. To sai dai kuma sau dai-dai har biyu ana hobbasa da nufin kawo karshen matsalar sau biyun kuma ana fuskantar cikas sakamakon cin fuska ga 'ya'yan kungiyar a bangaren jami'an tsaron kasar ta Najeriya, abun kuma da ya sa wasu ke ganin da kamar wuya ga kwamitin ya kai ga iya yin nasara a cikin filin da wasu suka kai ga gwaji suka ce Allah ba da sa'a.

To sai dai kuma a cewar Kabiru Tanimu Turaki dake zaman shugaban kwamitin kuma ministan harkoki na musamman ga gwamnatin kasar za su gwada kuma suna fatan kaiwa ga fitar da kungiyar daga ramin buyar ta zuwa ga teburin na shawara.

Fatan samun yarda da aminci

Aminci hada bera da kyanwa a teburi guda ko kuma kokari na ganin bayan rikici dai, irin wannan karatu a baya ne ya kai ga jami'an tsaron kasar kame Abu Darda dake zaman daya daga cikin dan aiken kungiyar domin tattaunawa a garin Kaduna a shekarar bara.

Ko bayan batun na tabbatar da aminci dai akwai kuma ayyukan jami'an tsaron da ke ci gaba da kamfen din hare hare kan tungar 'yan kungiyar duk da gwamntin da ta ce ta ji ta gani ta kuma sauya domin tabbatar da kawo karshen rikicin.

PRESIDENT GOODLUCK JONATHAN SHAKING HANDS WITH A MEMBER OF THE COMMITTEE ON DIALOGUE AND PEACEFUL RESOLUTION OF SECURITY CHALLENGES IN THE NORTH, BARR AISHA WAKILI DURING THEIR INAUGURATION AT THE PRESIDENTIAL VILLA ABUJA ON WEDNESDAY (24/4/13). LEFT IS MRS ESTHER CONDA.
Hoto: DW/A. Ubale Musa

Wani harin da ya kai ga hallaka mutane kusan 200 a garin Baga dake iyaka a jihar Borno dai na ci gaba da sosa rai da ma dora ayar tambaya kan aniyar gwamnatin da ke magana hannun riga dsa aiyyukan jami'an tsaron ta.

To sai dai kuma duk da haka a fadar Ambassador Ahmed Jidda dake zaman sakataren gwamnatin Jihar Borno kuma dan kwamitin ba zai sanya gwiwa ta yi sanyi kan kokarin na tabbatar da zaman lafiya ba.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal