An rantsar da shugaban ƙasar Mali
September 4, 2013Talla
A lokacin da ya ke yin rantsuwar shugaban ya sha alwashin kare jamhuriya tare mutunta kudin tsarin mulki da kuma sa a yi aiki da shi. An dai zaɓi IBK ne mai shekaru 68 da haifuwa a cikin watan jiya a wani wa'adin mulki na shekaru biyar.
Tun da farko dai, sai da ka yi ban hannu na mulkin a safiyar yau tsakanin sabon shugaban da kuma shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya Dioncouda Traore. Babban ƙalubalen da ke a gaban shugaban shi ne na sake haɗa kawunan al'ummar ƙasar bayan yaƙin da ƙasar ta yi fama shi. Nan gaba ne ai a rana 19 ga wannan wata za gudanar da wani ƙasaitaccen bikin rantsar da shugaban a gaban shugabannin ƙasashen duniya.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh