1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rufe hukumomin gwamnati a Amurka

October 1, 2013

Sabani tsakanin 'yan majalisar Amurka dangane da kasafin kudi na shekara ta 2014, ya jagoranci tsayar da harkokin gwamnati a bangaren fadar gwamnati ta White House.

https://p.dw.com/p/19s2D
A stop sign is seen at dusk next to the US Congress building on the eve of a possible government shutdown as Congress battles out the budget in Washington, DC, September 30, 2013. AFP PHOTO/ MLADEN ANTONOV (Photo credit should read MLADEN ANTONOV/AFP/Getty Images)
Hoto: MLADEN ANTONOV/AFP/Getty Images

Fadar gwamnatin Amurka ta white house ta bada umurnin tsayar da tafiyar da harkokin gwamnati , sakamakon sabanin da aka samu tsakanin 'yan majalisa, daya jagoranci kin amincewa da kasafin shekara ta 2014 da Obama ya gabatar. Wannan dai shine karon farko da Amurkan ta fuskanci irin wannan yanayi cikin shekaru 17 da suka gabata. Shugaba Obama ya ce babu shakka rufe hukumomin zai shafi tattalin arzikin kasar.

Da misalin karfe tara da rabi agogon Amurkan ne dai, akesaran 'yan majalisar Dottijan kasar za su koma zama, a daidai lokacin da 'yan demokrats zasu yi watsi da gabatarwar 'yan majalisar wakilai na daukar nauyin kula da harkokin gwamnati. Tuni dai 'yan demokrat din suka yi gargadin cewar, tsayar da harkokin gwamnati, zai hana ma'aikata dubu 800 samun albashinsu, kana ya haifar da cikas a kokarin farfado da tattalin kasar.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu