1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sace tsohon Firaministan Libiya

August 14, 2017

'Yan tawaye a kasar Libiya sun yi awon gaba da wani tsohon Firaministan kasar Ali Zidan, wanda ya taba fuskantar makamancin wannan yanayin shekaru hudu da suka gabata.

https://p.dw.com/p/2iD9n
Ali Zidan, tsohon Firaministan kasar Libiya
Ali Zidan, tsohon Firaministan kasar LibiyaHoto: picture-alliance/AP Photo

Wasu 'yan tawaye a Libiya sun yi awon gaba da wani tsohon Firaministan kasar Ali Zidan. Shi dai Ali Zidan da ke zaune a Tripoli babban birnin kasar, ya shiga hannun 'yan tawayen ne lokacin da yake ganawa da wasu manyan jami'an tsaro. Akwai ma wadanda ke ganin mutanen na da alaka da magoya bayan bangaren gwamnatin kasar da Malisar Dinkin Duniya ya amince da shi.

Babu dai wani karin haske a hukumance kan waje ko halin da tsohon Firaministan na Libiya ke ciki. Cikin watan Oktoban shekara ta 2013 ma dai an taba yin garkuwa da Ali Zidan, kafin daga bisani aka sako shi.