1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saka lokacin zaɓen shugaban Aljeriya

January 17, 2014

Shugaban ƙasar Aljeriya ya saka hannu a kan ayar dokar da ke tabbatar da gudanar da zaɓen shugaban ƙasa

https://p.dw.com/p/1AsxA
Hoto: F.Batiche/AFP/GettyImages

Shugaban ƙasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya rantaɓa hannu a kan ayar dokar da ta amince da gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ranar 17 ga watan Afrilu mai zuwa. Shugaban ɗan shekaru 76 da haihuwa ya saka hannu jim kaɗan bayan dawowa daga ƙasar Faransa, inda aka duba lafiyarsa. Jam'iyya mai mulki ta zaɓe shi a matsayin ɗan takara, domin ya nemi wa'adi na huɗu na wasu shekaru biyar, amma har yanzu bai ce ya amince ba. Bouteflika ya shafe shekaru 15 ke nan yana mulkin ƙasar ta Aljeriya da ke yankin arewacin Afirka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane