1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake bude filin jirgin saman Sanaa a Yemen

Mohammad NasiruAugust 15, 2016

Kawancen sojojin kasashen Larabawa a Yemen ya amince da jigilar kayan agaji ta sama.

https://p.dw.com/p/1Jih4
Symbolbild Luftbrücke Westafrika Transall
Hoto: imago/Papsch

Kungiyoyin agaji na Majalisar Dinkin Duniya ka iya komawa amfani da filin jirgin saman babban birnin kasar Yemen wato Sanaa wajen jigilar kayan agaji ga 'yan kasar mai fama da yakin basasa. Yanzu haka dai an sake bude filin jirgin saman don saukar da kayan agaji.

A ranar Talata da ta gabata kawancen sojoji karkashin jagorancin kasar Saudiyya suka rufe filin jirgin saman, bayan da suka fara kai farmaki ta sama kan wuraren 'yan tawayen Houthi da masu mara musu baya na rundunar sojojin kasar. Sojojin 'yan Houthi din ne ke iko da babban birnin kasar da kuma wani yanki mai girma da ke arewaci.

Tun a watan Maris na 2015 kawacen sojojin da Saudiyya ke wa jagora, ke tallafa wa dakarun shugaba Abd Rabbo Mansur Hadi. Yunkurin baya bayan nan na samar da zaman lafiya karkashin Majalisar Dinkin Duniya ya ci-tura.