1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saki dan Tunusiya da aka kama kan harin Berlin

Gazali Abdou Tasawa
December 29, 2016

Mahukuntan shari'a a Jamus sun saki mutuman nan dan asalin kasar Tunusiya da ake tsare da shi a bisa zargin kasancewa da hannunsa a cikin harin ta'addancin da aka kai da babbar mota a kasuwar Kirsimetin birnin Berlin. 

https://p.dw.com/p/2V1ap
Deutschland Sicherheit Sylvester
Hoto: Reuters/F. Bensch

Kakakin hukumar shari'a ta kasar ta Jamus Frauke Köhler wacce ta sanar da labarin ta ce, sun saki mutumin dan shekaru 40 bayan da bincike ya wanke shi tare da cewa ba shi da alaka ko miskala zarratun da Anis Amri dan Tunusiyar mai shekaru 24 da aka kashe a ranar Jumma'ar da ta gabata a kasar Italiya da kuma Jamus ta bayyana a matsayin wanda ya kaddamar da harin na birnin Berlin na ranar 19 ga watan Disambar nan da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12. 

Frauke Köhler ta kara da cewa sakamakon binciken nasu na baya ya tabbatar da cewa, Lukasz Urban direban motar na asali dan kasar Poland da aka iske gawarsa a cikin motan bayan harin, yana mace lokacin da aka kai harin.