1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saki Hosni Mubarak daga gidan yari

August 22, 2013

A dazu ne aka sallami tsohon shugaban Masar Hosni Mubarak daga gidan yarin da ake tsare da shi bayan da aka gurfanar da shi gaban kuliya bayan da aka kau da gwamnatinsa.

https://p.dw.com/p/19UsU
FILE - In this Tuesday, Feb. 8, 2011 file photo, the Egyptian President Hosni Mubarak sits during his meeting with Emirates foreign minister, not pictured, at the Presidential palace in Cairo, Egypt. Egypt’s state news agency says the country’s top prosecutor has ordered ousted President Hosni Mubarak be detained for 15 days pending investigation into a new case of corruption by him and his family for pocketing state funds slated for the presidential palaces. Mubarak, 84, in detention since April 2011, is currently held in a military hospital because of health issues. (AP Photo/Amr Nabil, File) /eingest. sc
mubarak ägypten justiz kairo hausarrestHoto: AP

Sallamar ta Mubarak dai ya biyo bayan umarnin da babban mai gabatar da kara na kasar ya bada da safiyar yau, inda ya ce a sallame shi tunda alkalan da ke masa shari'a sun ce ba za su cigaba da tsare shi ba bisa tuhumar da ake masa.

Jim kadan bayan da aka sake shi, an dauke shi a wani jirgi mai saukar ungulu zuwa wani asibitin soji da ke birnin Alkahira don duba lafiyarsa inda nan gaba ne ake sa ran komawarsa gida.

Sai dai mahukuntan kasar sun ce zai kasance karkashin daurin talala in ya koma gida kasancewar akwai sauran shari'ar da zai fuskanta nan gaba.

Magoya bayan na Mubarak dai sun yi ta sowa a gaban gidan yarin Tora lokacin da aka sake.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamdou Awal