1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saki Paul Rusesabagina daga gidan yarin Rwanda

Ramatu Garba Baba
March 25, 2023

Mutum sama da dubu daya Mista Paul Rusesabagina ya yi nasarar karewa daga hallaka a lokacin tsananin kisan kiyashi mafi muni a tarihin kasar Ruwanda.

https://p.dw.com/p/4PEwL
Paul Rusesabagina
Paul RusesabaginaHoto: Imago Images/Belga/M. Maeterlinck

Fadar Washington a Amirka ta bayyana farin ciki da matakin gwamnatin Ruwanda na sakin Paul Rusesabagina daga gidan yarin da aka jima ana tsare da shi, sanarwar ta ce, an kwashi watanni ana tattaunawa kafin kasashen biyu su cimma yarjejeniyar da ta kai ga sakin Rusesabagina, mutumin da ya ceci dubban 'yan kabilar Tutsi da Hutu a lokacin kisan kiyashin da aka hallaka mutane dubu dari takwas a Ruwanda da ke yakin kahon Afirka. A sakamakon wannan bajintar ta wancan lokaci, masana'antar shirya fina-finan Amurka ta Hollywood ta shirya wani fim mai suna Hotel Ruwanda. 

Daga bisani bayan yakin, tsohon manajan Otel din, ya shiga takun saka da gwamnatin Paul Kagame da ya kira ta danniya tare da suka manufarta, amma an daure shi a shekarar 2019 bisa zargin mara wa kungiyar 'yan tawaye baya, lamarin da ya kai ga yanke masa hukuncin dauri na shekaru ashirin da biyar. A sakamakon daure shi, dangantaka a tsakanin Ruwanda da Amurka ta yi tsami.