1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sako malaman Kirista da aka sace a Kamaru

June 1, 2014

Hukumomin Kamaru da na kasar Italiya sun tabbatar da cewa turawan da aka sace a arewacin kasar Kamaru sun samu kubuta daga hannun wadanda suka sace su.

https://p.dw.com/p/1CABI
Papst Franziskus Ostermesse Rom Petersplatz Vatikan 20.4.2014
Hoto: Reuters

Ministan harkokin wajen kasar Italiya da kuma fadar Vatikan duk sun sanar da cewa an sako limaman Kirista 'yan kasar Italiya biyu da kuma wata 'yar kasar Kanada wadanda aka sace a kasar Kamaru. Mutanen uku an sace su ne a arewacin kasar ta Kamarun watanni biyu da suka gabata. Shi ma dai ministan sadarwan kasar Kamaru Issa Tchiroma Bakary, ya tabbatar wa manema labarai sakin wadannan turawa biyu wadanda ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka sace su, a kusa da kan iyakar Najeriya da Kamerun. Ministan harkokin wajen Italiya ya mika godiyarsa ga kasar Kanada da Kamaru bisa kokarin da suka yi na sako malaman na addinin Kirista. Amma bai yi wani karin haske ba bisa yadda aka yi mutanen suka kubata.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasir Awal