1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sami ci gaba a fannin kiwon lafiyar yara

September 13, 2013

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yawan mace-mace na yara 'yan ƙasa da shekaru biyar a duniya ya yi ƙasa da kusan kishi 50 cikin ɗari.

https://p.dw.com/p/19gv6
A young girl tries to engage Soa Tamba (5) in play at THINK's transit centre for children in contact with law in Monrovia, the capital of Liberia. Soa, mentally challenged from birth, was found abandoned at the door of a hospital three years ago. The case was reported to the police who brought him to THINK. In recent times, Liberia continues to recover from a ruinous 14-year civil war that ended in 2003. Although the Government is working to rebuild the country‚Äôs destroyed infrastructure, many Liberians still live without access to basic services. The influx of approximately 178,000 refugees from Cv¥te d'Ivoire, who fled their own country after controversy surrounding the 28 November 2010 presidential election turned violent, has only exacerbated the situation. Waning supplies of safe drinking water and food, inadequate sanitation facilities, constricted access to medical care and overcrowding all threaten the health of Liberian and Ivorian children alike. The education of many children has also been disrupted because refugees stay in schools when there are not enough families to host them. The poor condition of roads makes it difficult for aid to reach remote areas, where many of the most vulnerable families live. Many of the refugees have returned home, but thousands have stayed back, often hosted by Liberian communities and families, both in rural and urban areas of the country. NGOs and the Liberian Government continue to work hard to provide life-saving services for both Liberian citizens and Ivorian refugees.
Hoto: picture-alliance/AP Images

Lisafin dai ya yi daidai da rabi na yawan yaran da ke mutuwa a duniya tun daga shekarun 1990. Duk da ma cewar a kowace rana yara 'yan ƙasa da shekaru biyar dubu 18 ke mutuwa.

A cikin wani rahoto na haɗin gwiwa da ƙungiyar lafiya ta duniya WHO ko kuma OMS da UNICEF  da kuma bankin duniya suka wallafa a yau, sun ce ana kan hanyar rage  mace-macen yara da kishi biyu bisa uku kafin  nan da shekarun 2015.

Rahoton ya ce yawancin mace-mace na yara na faruwa ne a cikin ƙasashen  Kwango da Pakistan da China da Indiya da kuma Najeriya ƙasashe biyu na ƙarshe inda lamarin ya fi yin ƙamari.

Yawanci ana samu mutuwar yara  ne wajen haifuwa da sauran cututtuka irinsu gudawa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita        : Usman Shehu Usman