1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nnamdi Kanu ya baiyana a Isra'ila

Ramatu Garba Baba
October 23, 2018

Kungiyoyin fafutuka da sauran al'umma a yankin da 'yan kabilar Igbo ke zaune a Najeriya na ci gaba da samun rarrabuwar kawuna kan Nnamdi Kanu da sahihancin fafutukarsa ta girka kasar Biafra ta 'yan kabilar Igbo zalla.

https://p.dw.com/p/371DH
Nigeria Biafra | Nnamdi Kanu
Hoto: DW/K. Gänsler

Yanzu rikici ne ya barke a tsakanin magoya bayan shugaban kungiyar rajin kafa kasar Biafra ta IPOB, Nnamdi Kanu tun bayan da ya baiyana a Isra'ila. A baya bayan nan dai,Kungiyar Biafra ta asali a yankin wato MASSOB ta fito fili ta la'anci takidin na shugaban IPOB cewa fafutukarsa ba ta kafa Biafra ba ce.

Kanu da ya tsere daga Najeriya tun bayan wani atasayen dakarun sojin Najeriya na ''Python Dance'' wato rawar Damusa a yankin na Igbo, aka nemi shugaban na kungiyar da gwamnati ta ayyana a matsayin haramtacciya, an yi ta rade-radin an kashe shi abin da ya haifar da cece ku-ce mai yawa musamman a daukacin yankin na Igbo.

Kwatsam sai aka ji duriyarsa a Isra'ila, inda ma a wani jawabi da ya gabatar ga dimbin magoya bayansa da ke sassan duniya musamman wadanda suke  a Najeriya, ya tabbatar musu cewar fafutukar kafa kasa mai 'yancin kanta ta Biafra tana nan, kuma nan ba da dadewa ba zai sauka a Najeriyar, don ci gaba da wannan fafutuka, sannan ya yi kira ga al'umar Igbo da su kauracewa zabukan  kasar na 2019 da ke tafe gami da kafewa kan dole ayi kiran taron kasa wato Referendum.

Amma bayan bayyanar ta Nnamdi Kanu, sai akai ta samun rarrabuwar kanu a game da goyon bayan da ya saba samu a baya, inda wasu a yankin na Igbo ke ganin Kanu din ba da gaske yake ba kan batun na Biafra, sai dai kuma duk da haka akwai masu amanna da akidarsa. Yanzu Kungiyar IPOB ta rabe biyu, inda daya bangare da wani Mista Olisa Mbakwe ke jagoranta ya fara sabuwar adawa da Nnamdi Kanu, kuma dama kungiyar rajin san kafa kasar ta Biafra ta  asali MASSOB  a takaice ,ta bayyana Nnamdi Kanu din da cewar mayaudari ne,tare da kira ga kabilar Igbo da ta yi watsi da jawabin Nnamdi Kanu da ya yi ta kafafen watsa labarai.

Dama kuma, wata kungiyar matasa a yankin Igbo mai suna  East Renewal Group ta nuna yatsa ga Nnamdi Kanu din tun bayan bayyanar tasa,cewar kada ya sake ya tako kafarsa a kasar balle ma yankin na Igbo,domin matsawar tai ido biyu da shi,to lallai za ta damke shi tare da mika shi ga hukumomi a Najeriyar ,domin ta fahimci Kanu din matsoraci ne kuma mai dakile ci gaban kabilar ta Igbo.

Koda yake dai hukumomin Najeriya sun haramta takidin kungiyar ta rajin Biafra ta IPOB ,bayanai sun tabbatar da cewar har yanzu, 'yan kungiyar su kan gudanar da tarurruka da jerin gwano daga lokaci zuwa lokaci,wadda kuma hakan kan haifar da cin zarafin jama'a dama barnata dukiyoyi tare da salwantar rayuka.