1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu sabon shiga a Kwamitin Sulhu

October 18, 2013

Tarayyar Najeriya da ke yammacin Afirka ta samu damar zama mamba a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin duniya bayan ga kasashen Chadi da Saudiya da ke zama sabon shiga.

https://p.dw.com/p/1A1tj
Hoto: Reuters

Kasashen da suka samu amincewa daga yankunansu sun zama mambobin Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Inda kasashen Chadi, da Saudiya da kuma Lithuaniya suka samu shiga cikin kwamitin a karon farko. Akwai kuma kasashen Najeriya da Chile, wadanda aka zaba da suka samu shiga sau hudu kafin wannan lokaci.

Wannan ya zama karo na farko cikin shekaru masu yawa da babu takara. Sai dai yankunan na duniya suka gabatar da wadanda za su wakilce su. Ranar daya ga watan Janairu na shekara mai zuwa ta 2014, kasashen za su fara wa'adin cikin kwamitin sulhun na Majaliasar Dinkin Duniya mai wakilai 15, har zuwa karshen shekara ta 2015.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe