1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Mozambik

August 25, 2014

Gwamnati karkashin Frelimo da babbar jam'iyyar adawa ta Renamo sun amince da tsagaita wuta don wanzar da zaman lafiya a Mozambik mai arzikin karkashin kasa.

https://p.dw.com/p/1D0MF
Alte Waffen von RENAMO
Hoto: Fomicres

Bayan shekaru biyu ana gwabza fada, gwamnatin kasar Mozambik da babbar kungiyar adawa sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta. A Maputo babban birnin kasar aka cimma yarjejeniyar da tsohuwar kungiyar 'yan tawaye da yanzu ta rikide zuwa jam'iyyar adawa ta Renamo. Yanzu haka dai sannu a hankali mayakan Renamo za su mika makamansu sannan a rika shigar da su cikin rundunar sojin kasar. Har izuwa shekarar 1992 Renamo da jam'iyyar da ke mulki a yanzu ta Frelimo sun gwabza kazamin yakin basasa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin miliyan daya. Bayan yakin Renamo ta zama babbar jam'iyyar adawa a Mozambik, amma ta kasa cin zabe balantana ta kafa gwamnati. Shekaru biyu da suka gabata fadan ya sake barkewa bayan gano sabbin arzikin karkashin kasa na kwal da kuma iskar gas.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe