1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shawo kan wutar daji a Portugal

Abdourahamane Hassane
July 27, 2017

'Yan kwana-kwana masu aikin kashe gobara a Portugal sun yi kokarin shawo kan wutar dajin da ta haddasa mumunar barna.

https://p.dw.com/p/2hGzV
Portugal Waldbrände zu 95 Prozent unter Kontrolle
Hoto: Reuters/R. Marchante

Wutar dajin wacce ta yi kwanaki biyar tana ci da karfin gaske a yankin tsakiya na kasar, a yanzu wani babban jami'in gwamnatin da ke kula da ayyukan jin kai ya ce karfin ta ya rage kishi 90 cikin dari. Musammun ma a agarin Serta da ke cikin jihar Castelo Branco inda aka baza 'yan kwana-kwana  1200 tun ranar Lahadin da ta wucce.