1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shiga shekaru na 10 da aukawa Iraki

March 20, 2013

A shekara ta 2003 ne dakarun kasa da kasa a karkashin jagorancin Amirka suka aukawa kasar Irki a wani matakin kifar da gwamnatin Saddam Hussein da ake zargi da mallakar makaman guba

https://p.dw.com/p/180lr
Hoto: AFP/Getty Images

A kwana a tashi bana shekaru 10 kenan daidai da aukawa kasar Iraki, a lokacin da dakarun kasa da kasa a karkashin jagorancin Amirka suka kaiwa kasar hari bayan da suka zargi gwamnatin Saddam Haussein da mallakar makaman kare dangi.
Ana dai wadannan shugulgullan ne a kasar ta Iraki cikin tsauraran matakan tsaro da kuma zaman fargaba bayan da a jiya wani bam ya tashi inda ya hallaka kimanin mutane 52, yayinda sama da 170 suka samu raunuka.
Tun dai bayan kifar da gwamnatin Saddam tare da rataye shi yanzu haka gwamnatin shugaba Nouri Al Maliki na fuskantar manyan kalubale wadanda suka hada da na tsaro da kuma na siyasa hadi da riginginmun addini inda masu goyon bayan akidar Sunni ke yakar 'yan shi'a abinda ke dada kara tabarbarewar al'amuran tsaro.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Saleh Umar Saleh