1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soke dokar da ta janyo cece kuce a Masar

December 9, 2012

Shugaban ƙasar Masar Mohamed Mursi ya kawar da ayar dokar da ta bashi ƙarfi fiye da kima

https://p.dw.com/p/16ygv
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugaban Masar Mohamed Mursi ya kawar da ayar dokar da ta bashi ƙarfi fiye da kima, wadda ta janyo zanga zanga cikin yankunan ƙasar.

Soke ayar dokar ya biyo bayan ganawar da shugaban ya yi jiya Asabar da ƙungiyoyin 'yan adawa, wanda jiga jigan 'yan adawan ƙasar su ka ƙaurace. Duk da wannan matakin 'yan adawan na neman ganin soke gudanar da ƙuri'ar raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin da ake taƙaddama akai, wanda wakilan 'yan adawa su ka fice daga wajen rubutawa, saboda yadda 'yan ƙungiyar 'yan-uwa Musulmi ta shugaba Mursi, aka zarge su da saka wasu ra'ayoyi na kishin Islama.

Amma shugaban ya ce za a gudanar da zaɓen na raba gardama. Matakin na Shugaban ƙasar ta Masar na cin tuwon fashi, ya zo jim kaɗan bayan rundunar sojan ƙasar ta fitar da sanarwar neman ganin kawo ƙarshen rikicin ƙasar ta hanyar tattaunawa.

Mawallaf: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi