1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalaman Jonathan game da 'yan matan Chibok

Uwais Abubakar IdrisFebruary 12, 2015

Kungiyar #BringBackOurGirls ta nuna rashin jin dadinta da kalaman Shugaba Jonathan cewa za a sako 'yan matan Chibok nan gaba kadan.

https://p.dw.com/p/1EaIU
Nigeria Boko Haram soll offenbar entführte Mädchen freilassen
Hoto: Reuters/A. Sotunde

A Najeriya kalaman da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya yi na bada tabbacin cewa nan da 'yan makwani za a sako 'yan matan Chibok ya harzuka 'yan kungiyar #BringBackOurGirls da ke fafutukar ganin an sako 'yan matan tun lokacin da 'ya'yan kungiyar Boko Haram suka kamesu.

Tun a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ake fafutukar ganin an sako ‘yan matan na Chibok da aka sace, fafutukar da 'ya'yan kungiyar ta #BringBackOurGirls ke yi da bata kai ga cimma ruwa ba, duk kuwa da matsin lambar gangami da suka yi.

Fitowa fili da shugaban Najeriyar ya yi ya bayyana cewa batun sako ‘yan matan na Chibok lamari ne na ‘yan kwanaki kalilan musamman saboda aiki na hadin guiwa da a yanzu sojojin Najeriyar ke yi da na makwabtan kasashe irin su Jamhuriyar Njar, da Chadi da ma Kamaru ya sanya maida martani daga masu fafutukar da suke cike da fatan jin wani labari.

Ba sabon abu cikin kalaman Jonathan

Nigeria Goodluck Jonathan
Hoto: AFP/Getty Images

Abin da suka ce shiru ya fi irin kalaman na shugaba Jonathan. Mr Hosea Habana Tsambido shi ne shugaban kungiyar al'ummar Chibok mazauna Abuja da ke gaba-gaba wajen fafutukar.

"Tun yaushe ya yi ta magana cewa za a sako su nan kusa? Ni bana ma son in ji in ana magana a kai don shirme ne, don ai damuwa duka a Najeriya ne, sai munga abin da aka yi kafin mu fara fita mu yabe su. Ai dan kuturu sai ya girma da yatsu kafin ka yabe shi. In ba haka ba mutum ya yi magana daya sau biyu sau uku har sau shida babu cikawa. Sai ka saurare shi ka ce yana magana? Wallahi ni a gaskiya bana ganin yana magana."

Tsawon lokaci da ake dauka da ya jefa iyayen 'yan matan da dama cikin hali na rashin tabbas da dogara bisa dole a kan inda aka dosa, saboda abin da suka bayyana da rashin samun labarin 'ya'yan nasu. Abin da ya sanya sannu a hankali bayan sama da kwanaki 300 aka fara mance wa da batun.

To sai dai alwashi ko kyakkyawan fata irin wannan abu ne da za a yi fatan zai samar da sabon fata, har ma da karfafa guiwa bisa yadda batun ya fito daga shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan.

Nigeria Boko Haram soll offenbar entführte Mädchen freilassen
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Ko me ya sanya masu fafautukar suke jin babu wani canji da suka samu daga kalaman na shugaban Najeriya a kan wannan batu.

Akwai siyasa cikin zancen

Malam Auwal Musa Bashir na kungiyar ta #BringBackOurGirls ya ce akwai dalilan da ya sanya su haka.

"Ka ga dai yau kwanaki 308 kenan da muka fara kira ga gwamnatin Najeriya ta ga an sako 'yan matan nan kuma ai tun bayan kwanaki 15 da sace 'yan matan muka fara wannan gangami. Da farko ma dai gwamnatin ta ce ba ta yarda an sace 'yan matan ba sannan bayan kwanaki biyu ta ce an sace su an gano da yawa daga cikinsu. Kai ta ma zo ta ce ai ba a sace su ba. Amma ai gwamnati ce da ta saba yin abubuwa kuma ga shi a yanzu ana shirin yin zabe. Ka ga kenan in ka yi la'akari da abubuwan da suka faru a baya da halin da ake ciki yanzu to akwai abubuwa da yawa a kasa."

A yayin da ake sa ido ganin abin da zai biyo baya daga bayanan na shugaban Najeriya a kan 'yan matan na Chibok da kokarin yantar da su, ga Mallam Sani Aliyu na kungiyar kare hakoki na demukradiyya ya ce batu ne na siyasa kawai.

Bayanan da ake samu na aikin hadin guiwa da y a sanya sojojin Najeriyar gudanar da sintiri ta sama a kan dajin Sambisa inda aka dade da hasashen 'yan matan na can, tuni kungiyar kare hakin jama'a ta Amnesty International ta yi gargadi a yi hankali da afka wa 'yara da aka yi garkuwa da su. Har zuwa wannan lokaci lamari sace 'yan matan Chibok na zama wanda ya fi daukan hankali a matsalar kai hare-hare da sace jama'a a yankin na arewa maso gabashin Najeriya.