1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soma taro kan Ebola a birnin Geneva

August 6, 2014

Kwamitin gaggawa mai kula da tsarin kiwon lafiya na hukumar WHO, ya fara zaman taronsa na kwanaki biyu a birnin Geneva kan annobar cutar Ebola.

https://p.dw.com/p/1CpeS
Dr Margaret Chan
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan kwamiti dai, zai tantance ko wannan cuta za ta shiga sahun farko na kulawa a matsayin wata barazana ga kasashen duniya, inda a ranar Juma'a mai zuwa ake sa ran kwamitin zai sanar da sakamakon abun da ya cimma kan wannan batu.

Kwamiti da ke zamansa na farko kan cutar ta Ebola, ya samu halartar kwararru kan kiwon lafiya na duniya da sauran wakillan kasashen da abun ya shafa wadanda za su bada nasu ra'ayi na masana, tare kuma da babbar Daraktar hukumar Dr Margaret Chan.

Kawo yanzu dai wannan cuta, ta yi sanadiyar rasuwar mutane fiye da 900 a yammacin Afirka a wani adadi na baya-bayan nan da hukumar ta lafiya ta bayar. Yawan masu dauke da cutar ya kai mutum 1603 a cikin kasashen na yammacin Afirka, da suka hada da Guinea, Laberiya, Saliyo, da kuma Najejiya. Hukumomin a Najeriya dai sun sanar da kamuwar wasu mutane 7 da mutuwar mutun biyu sakamakon cutar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu