1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tabbatar da mutuwar mutane 37 sakamakon harin Tunisiya

Suleiman BabayoJune 27, 2015

Mahukuntan ƙasar Tunisiya na ci gaba da ɗaukar matakai bayan hari kan masu yawon buɗe ido

https://p.dw.com/p/1FoGy
Tunesien Sousse Terroranschlag
Hoto: Reuters/Z. Souissi

Mahukuntan ƙasar Tunisiya sun tabbatar da mutuwar mutane 37 cikin harin da aka kai kan masu yawon buɗe ido a garin Sousse. Ministan lafiya na kasar Saeed al-Abadi ya tabbatar da alƙaluman yayin hira da wata tashar rediyo.

Galibin waɗanda suka gamu da ajalinsu sun fito ne daga ƙasashen Jamus, da Birtaniya, da Belgium, da kuma Tunisiya kamar yadda ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta bayyana. Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-Moon ya yi tir da wannan farmaki na ƙasar Tuniya da ya hallaka mutane 37 da wanda aka kai Kuwait inda mutane 25 da suka mutu, da kuma wani harin ta'addanci a ƙasar Faransa da mutum guda ya hallaka.