1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsaida ranekun zaɓe a Russia

September 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuCY

A yau ne Shugaban ƙasar Vladmir Poutine, ya sa hannu a kan dokar shirya zaɓɓuɓuka daban daban a wannan ƙasa.

Ranar 2 ga watan desember na wannan shekara za a gudanar da zaɓen yan majalisun dokoki, sannan a yi zaɓen shugaban ƙasa ranar 2 ga watan Maris na shekara ta 2008.

Nan da kwanaki 5 masu zuwa, za a fara yaƙin neman zaɓen yan majalisun dokoki.

Majalisar Douma ta ƙunshi jimilar yan majalisa 450.

Kudin tsarin mulkin ƙasar Russie ya haramtawa shugaba Poutine shiga takara karo na 3, a zaɓen shugaban ƙasa.

Shi da kansa shugaban, ya bayyana yin biyaya ga kudin tsarin mulkin, ya kuma yi alƙawarin da ba zai cenza shi ba.

Shugaba Poutine, ya ce zai bayyana ɗan takara da zai maraya wa baya a lokacin da ya dace.

Masu kula da harakokin siyasar ƙasar Russie, na hasashen cewar ɗan takara na shugaban ƙasa bai zai wuce Serguei Ivanov ba, ko kuma mataimakin Praminista Dmitri Medvedev.