1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsige wani jagora mai sukar Maduro

Ramatu Garba Baba
August 8, 2017

Kotun kolin kasar Banizuwela ta zartar da hukuncin daurin shekara daya da watannin uku ga Ramon Muchacho, magajin garin Chacao da ke adawa da mulkin shugaba Nicolas Maduro.

https://p.dw.com/p/2htRn
Venezuela / Caracas / Proteste / Demonstration
Hoto: picture-alliance/dpa

Wata sanarwar da kotun ta fitar ta ce baya ga hukuncin zaman gidan yarin, an kuma tsige mista Muchacho daga mukaminsa na magajin gari. Garin Chacao da ke karkashin yankin Caracas babban birnin kasar ta Banizuwela, ya kasance wajen da aka kwashe akalla watanni hudu ana gudanar da zanga-zangar adawa ga gwamnatin shugaba Maduro.

Kotun dai ta ce ta sami magajin garin ne da laifin nuna halin ko-in-kula a rikicin da ya yi sanadiyar rayukan mutane da kuma ya haifar da tashin hankali na tsawon lokaci a kasar. A wannan Talatar ma dai sashen kula da hakkin bil'adama a Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga gwamnatin shugaba Maduro da ta gaggauta gudanar da bincike kan zargin cin zarafin al'umma sakamakon rikicin kasar da kuma bukatar sakin wadanda ake tsare da su ba bisa ka'ida ba.