1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tura karin sojojin Afghanistan zuwa yankin Helmand

Mohammad Nasiru AwalDecember 23, 2015

'Yan Taliban na ci gaba da dannawa tsakiyar lardin da ke fama da rigingimu yayin da mazauna kuma ke tserewa daga gumurzun da ake yi.

https://p.dw.com/p/1HSZB
Afghanistan Kämpfe in der Prozinz Helmand
Hoto: Getty Images/AFP/N. Mohammad

A wannan Larabar an tura karin dakarun Afghanistan yankin Helmand bayan da Taliban ta kame wasu wurare a yankin da ake noman ganyen opium ciki. Hakan ya sa a karon farko cikin watanni 14 an sake girke dakarun Birtaniya a lardin mai fama da rikici. Mazauna da ke tserewa daga yankin sun ce mayakan Taliban na kashe sojojin da suka kama yayin da 'yan Taliban din ke kara dannawa tsakiyar lardin. Yanzu haka dai ana kara nuna fargabar cewa lamuran tsaro za su tabarbare a yankin. Mukaddashin gwamnan Helmand Mohammad Jan Rasoolyar ya fada wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa an gaggauta tura karin dakarun gwamnati don karfafa guiwar 'yan sanda da sojojin da aka yi wa kawanya a tsakiyar lardin.