1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yanke hukuncin kisa akan wani tsohon jamiin mulkin soji Habasha

December 9, 2005
https://p.dw.com/p/BvHG

An yanke hukuncin kisa akan wani memba na tsohuwar gwamnatin mulkin soji ta kasar Habasha,saboda hannu da yake da shi a kisan wasu mutane fiye da 900 a lokacin mulkinsu.

Kotu ta dorawa tsohon gwamnan ,manjo Melaku Tefera laifukan kisan kiyashi da kuma wulakanta jamaa.

Babbar kotun ta kama shi da kashe mutane 971 da kuma lahanta wasu 83 a lokacinda yake gwamna a lardinGondar a arewa maso yammacin Habasha.

Wannan hukunci da aka yankewa Melaku,wani bangare ne na shariar da ake sauraro yau shekaru 11 ke nan,na wasu jamian gwamnatin mulkin sojin Habasha su 37 da suka yi mulkin kama karya a zamaninsu.

Ana kuma zarginsu da laifuka 209.

Karkashin dokokin kasar habasha ba zaa aiwatar da wannan hukunci ba har sai shugaban kasa ya amince.