1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yanke wa tsohon shugaban Masar hukunci

Muntaqa AhiwaApril 21, 2015

Kotu a kasar Masar ta yankewa tsohon shugaban kasar Masar Mohammed Morsi hukunci shekaru 20 bisa samunsa da ta yi da laifin tunzura jama'a ga yin bore.

https://p.dw.com/p/1FBUe
Mohammed Mursi
Hoto: STR/AFP/Getty Images

A yau Talata ne tsohon shugaban kasar Masar Mohammed Morsi zai gurfana gaban kotu don sanin matsayinsa kan zarge-zargen kashe masu zanga-zanga a kasar shekaru uku da suka gabata da ake yi masa.

Zaman kotun na yau Talata dai zai tabbatar da ko zargin Morsi na kashe masu zanga-zanga a shekara ta 2012 lokacin da yake karagar mulki, hukuncin da kuwa ake ganin zai iya zama na kisa ne.

Shugaba Morsi dai ya dare kan kujerar mulki bayan da guguwar neman sauyi ta yi waon gaba da shugaba Hosni Mubarak na Masar din a shekara ta 2011. Sannan kuma ya fuskanci juyin mulki daga wanda ya nada a matsayin babban hafsan hafsoshin kasar wato Abdul fatah Al Sisi da ke jagorantar kasar a halin yanzu, a shekara ta 2013, bayan wani bore mai karfi daga alumomin kasar.