An yi garkuwa da wani dan Amirka a Nijar
October 27, 2020Da yake magana da manema labarai Ibrahim Abba Lelé kantoman jihar Konni mai makwabtaka da Najeriya, ya ce mutanen da ba a san ko su waye ba sun sace mutumin wanda ya jima a yankin yana rayuwa da iyalinsa a wata gona da ke wajen kauyen na Masallata, sai dai ba a yi wani karin haske kan inda masu garkuwa da shi suka dosa ba.
A cikin watan Oktoban 2016 wasu ‘yan bindiga sun yi sace wani dan Amirka mai aikin jin kai Jeffery Woodke a garin Abalak, daga bisani suka garzaya da shi zuwa kasar Mali, sai dai a shekarar 2019 shugaban kasar Mouhamadou Issoufou ya tabbatar da cewa mutumin na na a raye.
A cikin watan Agustan da ya gabata ma dai kungiyar IS ta dauki alhakin kisan wasu Faransawa shida a wani wurin yawon bude ido na garin Koure mai tazarar kilomita 60 daga birnin Yamai.