1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a karrama musulmi a New Zealand

Abdullahi Tanko Bala
March 20, 2019

Firaministar New Zealand Jacinda Ardern ta ce za a gudanar da adduo'i na musamman ga muslmin da suka rasu a harin da wani dan bindiga ya kai wasu masallatai biyu a birnin Christchurch.

https://p.dw.com/p/3FL6z
Neuseeland, Christchurch: Beerdigung der Opfer
Hoto: Reuters/J. Silva

A kasar New Zealand  a wannan Laraba an gudanar da jana'izar ta farko ta mutanen da ka aka kashe  a harin ta'addanci da wani dan bindiga ya kai wasu masallatai biyu a Christchurch.


An yi Jana'izar wani dan gudun hijira dan kasar Siriya Khaled Mustafa tare da dan sa Hamza mai shekaru goma sha biyar. Dan uwansa wanda ya tsira da rauni a harin ya halarci jana'izar a kujerar guragu.


Daruruwan jama'a suka suka halarci jana'izar cikin jimami da alhini. Firaministar kasar Jacinda Ardern ta ce za yi shiru na mintuna biyu ranar Juma'a a fadin kasar domin addu'oi ga mamatan. Sannan za a yada kiran sallah kai tsaye a kafofin yada labarai domin karrama mamatan