1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi wa mai shari'ar Amirka da ban-kwana

September 25, 2020

An kwantar da gawar marigayiyar babbar mai shari'ar nan ta Amirka, Ruth Bader Ginsburg, domin yi mata gani na ban kwana tare ma da karrama ta da lambar yabo mafi daraja.

https://p.dw.com/p/3j1Oe
USA, Washington I Aufbahrung Richterin Ruth Bader Ginsburg
Hoto: Andrew Harnik/AP/picture-alliance

Ruth Bader Ginsburg, wadda ta rasu a makon jiya tana matsayinta na babbar mai shari'a a kotun kolin kasar, ta rasu ne tana da shekaru 87 a duniya bayan ta fama da cutar daji.

Ta kasance mace ta farko kuma Bayahudiya da ta taba shiga cikin rukunin mashahuran mutanen da ake karramawa da wannan matsayi a Amirkar.

Marigayiyar ta sha jinjina a lokacin da take raye a kan tsayawa kan hakkin mata da ma shaharar da ta yi a matsayinta na malamar makaranta kuma alkaliya.

A tarihin Amirka dai mutane 30 ne kacal aka taba yi wa irin wannan ban kwana da girmamawa a fadar shugaban kasa.