1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Kotu ta yi watsi da karar Mahama

Abdoulaye Mamane Amadou
March 4, 2021

Madugun 'yan adawar kasar Ghana da ya sha kaye a gaban kotu bayan da ya kasa samar da hujjojin kalubalantar sakamakon zaben Nana Akufo-Addoa matsayin shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/3qE8V
Afrika Ghana Präsidentschaftswahlen
Hoto: Xaume Olleros/AA/picture alliance

Kotun ta ce bangaren John Mahama da ke zargin an tafka magudi a yayin zaben, bai gabatar da wasu kwararan hujjojin da suka gamshi kotun ba, da zai sa har ta sake kiran wani sabon zaben shugaban kasa, saboda hakan kai tsaye ta yi watsi da karar.

Ba tun yau ba ne mutanen biyu da kowannensu ya shugabanci kasar Ghana ke ta ja in ja kan batun lashe zaben shugaban kasa, a kasar da ke da matukar tasiri a fagen dimukuradiyyar yankin yammacin Afirka.