1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zaɓi shugaban Ghana a matsayin jagoran ECOWAS

March 29, 2014

A ƙarshen taron da suka yi a birnin Yamoussoukro shugabannin ƙasashen yammacin Afirka sun zaɓi John Dramani Mahama a matsayin shugaban ECOWAS ko CEDEAO.

https://p.dw.com/p/1BYOY
Hoto: Getty Images /AFP

An zaɓi shugaban ƙasar Ghana John Dramani Mahama a matsayin sabon shugaban Ƙungiyar Gamayya Tattalin Arziki ta Ƙasashen Yammacin Afirka wato ECOWAS ko kuma CEDEAO. Mista Dramanin mai shekaru 55 da haifuwa wanda ya gaji Alassane Ouattara a kan matsyin an zaɓe ne shi a ƙarshen taron Ƙungiyar ta CEDEAO karo na 44 da ya gudana a birnin Yamoussoukro na Cote d'Ivoire.

Dramani ya zo ne a kan karagar mulkin a cikin watan Yuli na shekara 2012 bayan mutuwar John Atta Mills na Ghana. Ƙungiyar ta CEDEAO wacce ta ƙunshi ƙasashe 15 na yammacin Afirka na da yawan al'umma miliyan 300 masu magana da harshen Farasanci da Turancin Ingilishi da kuma yaren Portugal.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe