1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi Li a matsayin Premiyan China

March 15, 2013

'Yan majalisar China kimanin 3,000 ne suka kada kuri'unsu na amincewa da Li Keqiang domin maye gurbin Wen Jiabao.

https://p.dw.com/p/17ya1
BEIJING, CHINA - MARCH 15: China's newly-elected Premier Li Keqiang (L) shakes hands with former Chinese Premier Wen Jiabao near Chinese President Xi Jinping (R) during the fifth plenary meeting of the National People's Congress at the Great Hall of the People on March 15, 2013 in Beijing, China. Li Keqiang was elected as China's Premier Friday at the 12th National People's Congress, the country's top legislature. (Photo by Feng Li/Getty Images)
Hoto: Getty Images

A wannan Juma'ar ce majalisar dokokin kasar China ta zabi Li Keqiang a matsayin Premiya a hukumance, domin shugabantar wannan kasa ta biyu a bunkasar tattalin arziki. Kamar yadda ake zato wakilan fitacciyar jam'iyyar NPC, sun zabi Li mai shekaru 57 da haihuwa da murya daya, domin maye gurbin Wen Jiabao. Kusan wakilai 3, 000 suka taru a babban dakin taron birnin Beijing, domin zaben Li, wanda ke tabbatar da mataki na karshe na sauya madafan iko. 'Yan majalisar china din uku ne kadai suka kada kuri'ar nuna adawa, a yayin da wasu shida suka ki kada kuri'unsu. A yayin da shugaba Xi Jinping zai kasance jagorar kasar, Li zai shugabanci majalisar wakilai, tare da kula da gudanarwar gwamnati da fannin tattali. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta kasance shugabar gwamnatin wata kasar ketare ta farko da ta kira Li, domin taya shi murna. Kazalika sun tattauna matsalolin tattalin arziki dake addabar wasu kasashen Turai.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman