1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi sabon Firaminista a Afirka ta Tsakiya

August 10, 2014

An sanar da nadin Mahamat Kamoun a matsayin sabon Firaministan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, a wani mataki na kokarin kafa gwamnatin hadaka a wannan kasa.

https://p.dw.com/p/1CsDR
Hoto: Guy-Gervais Kitina/AFP/Getty Images

Kamar yadda ta yi alkawari a jiya Asabar (09.08.2014) a gaban dumbun 'yan kasar da sukayi zanga-zangar lumana, Shugabar rikon kwaryar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Catherine Samba Panza, ta nada Mahamat Kamoun wanda yake Musulmi ne, a matsayin sabon firaministan kasar wanda ya maye gurbin Andre Nzapayeke da ya yi murabus dan b ada damar kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa kamar yadda aka tanada a yarjejeniyar birnin Brazzaville.

Sabon Firaministan Kamoun masanin tattalin arziki ya kasance a matsayin mai ba da shawara a fadar shugabar kasar ta rikon kwarya, sannan kuma ya rike manyan mukamai gwamnati. Wannan nadin dai ya zo ne makonni biyu bayan yarjejeniyar ta Brazzaville da aka cimma a karshen watan Yuli da ya gabata, inda masu lura da al'ammura, ke ganin sabon Firaministan Mahamat Kamoun yana da babban aiki, na neman kara hada kan 'yan kasar da mafi yawa suka nuna kosawa da halin tashe-tashen hankulan da kasar ta fuskanta.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo