1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi shugaban hukumar Tarayyar Turai

Usman ShehuJuly 15, 2014

Fitaccen dan siyasa a Turai Jean-Claud Juncker, banasarar zabensa ya bayyana sabbin matakan da zai dauka na farfado da tattalin arzikin kungiyar ta EU

https://p.dw.com/p/1Cde7
CDU Bundesparteitag in Berlin (Jean-Claude Juncker)
Jean-Claud JunckerHoto: picture-alliance/dpa

Dan shekaru 59 da haifuwa Jean-Claud Juncker, ya samu kuri'u daga dukkan bangaren jam'iyyun da ke a majalisar, kama daga bangaren masu sassaucin ra'ayi da ku ma 'yan mazan jiya. Sabon shugaban ya bayyana man'yan ayyukan da zai sa a gaba cikin wa'adin mulkinsa.

"Zan gabatar da shawar daukan gagarumin shirin samar da zuba jari. Daga nan izuwa watan biyu na badi, wannan gagarumin shirin na zaburar da tattalin arziki da kuma bada damar yin gogayya shi zan gabatar. Ina fatan nan da shekaru uku masu zuwa, mu tara Euro biliyan 300, badon komai ba sai kawai musamman domin kamfanoni masu zaman kanmsu su samar da zuba jari"

Tun da farko gabanin zabensa, an zaci samun wani gagarunmin sauyi a kungiyar Tarayyar Turai, to amma sabon shugaban hukumar yace, burinsa shi ne ci-gaba da dinkewar Turai.

Mini-Gipfel in Schweden (Rutte, Merkel, Reinfeldt und Cameron)
Wasu shugabannin kasashen EUHoto: Reuters

"Babu batun wani juyin-juya hali ko akasin yin-juya hali a Turai. Zan bar Tarayyar Turai kamar yadda ta ke"

Jean-Claud Juncker ya nuna damuwarsa kan yadda Tarayyar Turai ta samu koma baya, bisa wasu al'amura da ya bayyana dalilai kamar haka.

"A matsayinmu na Tarayyar Turai an san mu da yin gogayya a duniya, mun samu koma baya ne, sabo da rashin yin hobbasa"

Shi dai sabon shugaban hukumar ta Tarayyar Turai, shi ne shugaban wata gwamnati da yafi kowa dadewa yana aiki cikin kungiyar ta EU. Inda shekara ta 1989 izuwa shekara ta 2009 ya ke rike da mukamin ministan kudi, kana daga shekara ta 1995 izuwa shekara ta 2013 ya kasance Firaministan kasarsa ta haifuwa wato kasar Luxemburg. Har ila yau daga shekara ta 2005 izuwa shekara ta 2013, Juncker ya kasance shugaban kungiyar kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Sulaiman Babayo