1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An Zargi Assad da amfani da makami mai guba

Ramatu Garba Baba
October 27, 2017

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun ce dakarun da ke biyayya ga shugaban Siriya Bashar al-Assad ne suka kai hari da makami mai guba da ke dauke da sinadarin Sarin a wani gari da ke kusa da birnin Damascus.

https://p.dw.com/p/2maps
Syrien Idlib Giftgasangriff
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS/Syria Civil Defence

Rahotanni sun ce harin ya yi sanadin rasuwar mutane akalla 87 sai dai hukumomi na Damascus da kuma gwamnatin Rasha da ke dasawa da shugaba Assad sun ce 'yan tawaye ne ke da alhakin kai harin amma kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce bayanan da ta samu bayan kammala bincike ya nuna cewar dakarun gwamnati ne suka kai harin.

Sakamakon wannan binciken da kuma martanin Amirka ta bakin sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson kan batun ya haifar da shakku kan yiwuwar yin wani zama a watan gobe don tattaunawa kan shirin wanzar da zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta.