1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi jami'an tsaro da kisan farar hula a Borno

April 22, 2013

A tarayyar Najeriya hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane 185 a wani gumurzu da aka yi tsakanin jami'an tsaro da yan kungiyar Boko Haram ne a karamar hukumar Baga dake jihar Borno

https://p.dw.com/p/18KpA
Hoto: Reuters

A tarayyar Najeriya hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane 185 a wani gumurzu da aka yi tsakanin jami'an tsaro da wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan gwagwarmayar kafa shari'ar musulunci da ake kira Boko Haram ne a karamar hukumar Baga dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar. Wannan rikici wanda aka faro shi ranar Juma'a da dare an dauki tsawon awanni kafin lafawar sa, kamar dai yadda wani jami'ain karamar hukumar Baga Lawan Kole ya shaidawa tawagar gwamnan jihar Borno Kashim Shatima wanda je ziyarar ganewa idon abinda ya faru.

Jami'in ya shaidawa gwamnan cewa sun bunne gawawwki da yawan su ya zarce 185 bayan da kura ta lafa, inda kuma aka kone gidaje da shaguna sama da dari da ababan hawa masu yawan gaske, abinda yasa tilas wasu mazauna garin suka tsere daga gidajen su.

Da yake karin haske kan wannan fadan, wani jami'in Soji Brig. Gen. Austin Edokpaye ya shaidawa tawagar gwamnan cewa maharan sun yi amfani da manyan rokoki gami da gurneti yayin wannan fada, inda kuma ya bada tabbacin cewa maharan sun shige daji amma zasu farauto su. Sai dai babu takamaiman bayani dake nuna cewa ga wanda ya hallaka fararen hular, inda wasu mazauna garin ke zargin jami'an tsaron da harbin kan-mai-uwa-da-wabi akan fararen hula, abinda jami'an tsaron suka musunta.

Nigeria Terror Leiter der Terrorgruppe Boko Haram Sektenführer Imam Abubakar Shekau
Imam Abubakar ShekauHoto: AP

Wannan yasa kungiyoyin fararen hula su bayyana damuwa da mamakin yadda za'a yi fada tsakanin bangarori biyu dake amfani da makamai amma fararen hula ne zalla zasu mutu inda kuma suka bukaci gwamnatin ta gudanar da bincike don gano matsalar da ta sa aka kashe fararen hular. Abdullahi Muhammad Inuwa, daya daga jami'an kungiyar kare hakkin Bani Adama da muhalli ne a tarayyar Najeriya. A ganin wasu talakawa da na zanta da su, da Lauje cikin nadi saboda haka suka bukaci a gudanar da bincike saboda zargin da suke yi na cewa jami'an tsaro ne suka hallaka fararen hular.

Wannan kisan kiayshi dai na zuwa kwanaki kalilan bayanda gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa kwamiti kan shirin yin afuwa ga ‘yan gwagwarmayar, abinda yasa wasu masharhanta ke ganin wata makarkashiya gwamnatin ta shirya don gurgunta shirin shi kansa. Malam Umar Adamu shugaban kungiyar Malami ta Jami'ar jihar Gombe ya bani dalilin wannan tunani nasu.

Kashim Shettima, Gouverneur von Borno State, Nigeria
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima,Hoto: DW

"A baya mai dai ana zargin jami'an tsaron da yin irin wannan kisan kiyashi da sunan yaki da ‘yan Jama'atu Ahlis Sunnah Lidda'awati Wal Jihad wanda aka fi sani da Boko Haram amma babu mataki da aka dauka na ladabtar da wadanda suka yi hakan abinda ya sa wasu ke zargin da gangan ake wannan aika-aika"

Mawallafi: Al-Amin Suleiman Muhammad
Edita: Umaru Aliyu