1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi MDD da gazawa a Sudan ta Kudu

Usman ShehuApril 9, 2014

A cewar kungiyar bada agajin gaggawa ta Doctors Without Borders, an yi biris da 'yan gudun hijira a sansanonin da suka fake.

https://p.dw.com/p/1Bejg
Konflikt im Südsudan Flüchtlinge 17.01.2014
Hoto: Phil Moore/AFP/Getty Images

Kungiyar ta yi kakkausar suka ga MDD bisa yadda ta yi watsi da dubban 'yan gudun hijira da ke warwatse a Sudan ta Kudu. Kungiyar ta ce jami'an MDD sun yi biris da 'yan kasar Sudan ta kudu dauke da raunuka, wasu na yashe a gefen sansanin MDD yayinda suke fiskantar tarin ruwa ruwa, wanda kuma kan iya sa su kamu da cututtuka. Kungiyar ta ci gaba da cewa, kusan za iya kwatanta sansanin na MDD a matsayin wani ramin mutuwa, domin in ba an dau matakan gaggawa ba, to wani bala'in cuta na iya barkewa. Kungiyar ta Doctors Without Borders ta bayyana aikin MDD a Sudan ta Kudu a matsayin wani abun kunya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu