1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi ´yan Sunni da hannu a harin da aka kai a Bagadaza

December 12, 2006
https://p.dw.com/p/BuYC
FM Iraqi Nuri Al-Maliki ya zargi masu matsanancin ra´ayi na Sunni da magoya bayan tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein da hannu a mummunan harin bam da aka kai kan wata kasuwa da ke Bagadaza. Akalla mutane 60 daukacin su talakawa ´yan shi´a suka mutu sannan fiye da 150 sun jikata lokacin da wani dan kunar bakin wake ya ta da bam a motarsa bayan ya tukata cikin wani gungun leburori dake neman aiki a babban birnin na Iraqi. Wanna dai shi ne karo na 4 da kai hari a wannan wuri a cikin wannan shekara kadai.