1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yiwuwar hannun 'yan ta'adda a harin California na Amirka

Lateefa Mustapha Ja'afarDecember 5, 2015

Hukumar leken asirin Amirka FBI ta ce akalar binciken da ta ke gudanarwa dangane da harbe-harben da aka kaddamar a California ta sauya zuwa binciken ayyukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/1HHqW
Jami'an tsaro na ci gaba da bincike kan harin California
Jami'an tsaro na ci gaba da bincike kan harin CaliforniaHoto: Getty Images/AFP/S. M. Haffey

Ko da yake shugaban hukumar ta FBI James Comey ya bayyana a wani taron manema labarai cewa kawo yanzu basu tabbatar da alakar maharan da wata kungiyar 'yan ta'adda ba, inda ya ce:

"Wannan sabon bincike ne na aikin ta'addanci wanda FBI ke jagoranta. Dalilin hakan shi ne kawo yanzu bincike ya nunar mana da cewa maharan na da alaka da tsattsauran ra'ayi, kana akwai yiwuwar hannun kungiyar 'yan ta'adda daga wata kasa."

Jami'an 'yan sandan Amirkan dai sun bayyana yakinin cewa daya daga cikin maharan ta ayyana yin mubaya'a ga kungiyar 'yan ta'addan IS. Mutane 14 ne dai suka hallaka a yayin harbin kan mai uwa da wabi da ya afku a San Bernardino yayin bikin Kirsimeti da aka fara.