1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da kai harin bamabamai a Iraqi.

July 2, 2006
https://p.dw.com/p/Burx

A wata sabuwa kuma, wasu rahotannin da muka samu dazu-ɗazun nan, na nuna cewa a ƙalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu a unguwar Karradha da ke kudancin birnin Bagadaza, yayin da aka ta da bam cikin wata mota yau da safen nan, wajejen karfe 8 agogon Iraqi.

Wannan harin dai ya zo ne kwana ɗaya, bayan ta da wasu bamabaman da aka yi a unguwar Sadr Citya na birnin Bagadazan, mai yawan mabiya ɗariƙar shi’iti, inda a ƙalla mutane 66 suka sheƙa lahira sa’annan wasu ɗari kuma suka ji rauni. Duk da tsananta matakan tsaro a Iraqin tun makwanni ukun da suka wuce dai, har ila yau babu alamun jami’an tsaron ƙasar na cim ma nasarar fatattakar ’yan tawayen daga birnin.