1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da taimaka wa Philippines

November 12, 2013

Majalisar Ɗinkin Ɗuniya ta ƙaddamar da shirin taimaka wa Philippines inda guguwa ta yi mumunar ɓarna a wasu sassan ƙasar

https://p.dw.com/p/1AFsW
A resident inspects one of the statues at the U.S. General Douglas MacArthur shrine that fell at the height of super typhoon Haiyan last Friday in Palo, Leyte province in central Philippines November 12, 2013. REUTERS/Erik De Castro (PHILIPPINES - Tags: DISASTER ENVIRONMENT)
Hoto: Reuters/Erik De Castro

A wannan Talata Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da shirin tallafa wa mutanen da guguwa ɗauke da ruwan sama ta tagaiyara a Philippines, inda dubban mutane suka hallaka, yayin da wasu suka tagaiyara.

Wani kiyasin na majalisar ta nuna kimanin mutane dubu goma suka hallaka sakamakon lamarin a gari guda na Tacloban da ke Gundumar Leyte, kuma akwai yiwuwar alƙaluman za su ƙaru yayin da ake ci gaba da tantance asarar da guguwar ta haifar.Kusan mutane milyan 10, da ke zama kishi 10 cikin 100 na al'ummar ƙasar bala'in ya shafa, inda mutane kusan dubu 700 suka rasa gidajensu. Ƙasashen na bayar da gudunamawa, inda Amirka ta bayyana cewar ta ware miliyan 20 na dolla domin sayan kayayyakin agajin gaggawa da ake bukata, bayan da mahaukaciyar guguwa da ake wa laƙabi da Haiyan ta haddasa ɓarnar rayuka da kuma dukiyoyi a wannan ƙasa. Jamus ta tura da tawagar ƙwararru zuwa wannan ƙasa ta Phillipnes, tare da ware kuɗi domin sayan kayayyakin agajin gaggawa da ake buƙata.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane