1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwagwarmayar raba kayan agaji bayan girgizar kasa

Mohammad Nasiru AwalApril 29, 2015

Alkalumman baya bayan nan sun ce girgizar kasar mai karfin maki 7.8 a ma'aunin Richter ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da 5000.

https://p.dw.com/p/1FHNe
Nepal Erdbeben Kathmandu Proteste Polizei
Hoto: AFP/Getty Images/P. Lopez

A sabili da mawuyacin halin kai dauki bayan girgizar kasar da ta auku a kasar Nepal, an fara fuskantar barazanar gwagwarmayar raba kayan agaji tsakanin wadanda suka tsira daga wannan bala'i. Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da agajin gaggawa ya ce tuni an fara takaddama kan ruwan sha. A halin da ake ciki tawagogin agaji daga kasashe fiye 15 suna a kasar ta Nepal. Majalisar ta Dinkin Duniya da gwamnatin Nepal ke kula da ayyukan 'yan agajin. Ana matukar bukatar masu aikin tono gawarwaki da masu kakkafa tantuna ga asibitoci da kuma injunan samar da wutar lantarki. Alkalumman baya bayan nan sun ce girgizar kasar mai karfin maki 7.8 a ma'aunin Richter da ta auku a ranar Asabar ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da 5000, sannan kimkanin 10000 sun jikkata. Rahotanni daga birnin Kathmandu sun ce masu ceto sun gano wani da ransa da ya shafe sa'o'i 82 karkashin buraguzan gine-gine.