1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana gudanar da bukukuwan Kirismeti

Abdullahi Tanko Bala
December 25, 2017

Shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya bukaci karrama 'yan gudun hijira da kyautata musu yana mai cewa yin hakan ya na da babban lada a addinin Kirista,Paparoman ya bayana haka ne a albarkacin Kirismeti.

https://p.dw.com/p/2pubi
Vatikan - Papst Franziskus - Urbi et Orbi
Hoto: Reuters/A. Bianchi

Kiristoci a fadin duniya ke bukukuwan zagayowar ranar Kiristimeti, ranar da aka haifi Yesu Almasihu. Da yake jawabi yayin wani babban taron adduo'i a daren jiya Lahadi, shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya bukaci Kiristoci a fadin duniya kada su manta da muradun 'yan gudun hijira wadanda suka baro kasashensu sakamakon tashe tashen hankula.

Paparoman wanda shi ma kakanninsa 'yan gudun hijira ne daga kasar Italiya, ya shaida wa taron masu ibada a Cocin Saint Peters Basilica a birnin Rome cewa miliyoyin mutane wadanda ba a son ransu suka yi gudun hijira ba, sun baro dangi da 'yan uwa wadanda suke shaukin rayuwa tare da su. Yace karrama yan gudun hijira da kyautata musu kamala ce ta addinin Kirista.

Kiran na Paparoman na zuwa ne a daidai lokacin da aka sami barkewar sabon tashin hankali a yankin gabar yamma sakamakon ikrarin Trump na baiyana birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Yahudawa.

Shi ma da yake jawabi a taron adduo'i Archbishop Pierbattista PIzzaballa shugaban Mujami'ar birnin Kudus ya soki lamirin shugaba Trump yana mai cewa birnin Kudus birni ne na salama da zaman lafiya.